Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike, ya bayyana cewa ya riga ya yanke shawarar wanda zai goya masa baya a zaben shugaban kasa na 2027.
A hirar da aka yi da shi a shirin Politics Today na tashar Channels Television, Wike ya ce zai mara wa dan takara baya ne wanda zai tabbatar da ci gaban Najeriya tare da kare muradinta.
Ya ce wannan mataki nasa na nufin hana kasar dawowa baya.
Wike ya kuma jaddada cewa yana aiki ne domin ci gaban jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP).
Ya ce: “Idan ba a sanar da ni taron NEC ba, ina da cikakken hakki na kalubalanta, kuma babu wanda zai hana ni hakkina. Jam’iyyarmu za ta gana gobe domin mu tabbatar da adalci bai mutu ba. Babu wanda ya fi ni yi wa PDP hidima. Ni dan Najeriya ne kuma zan iya ba da gudummawa wajen cigaban kasar nan.”
Zaben Shugaban Kasa 2027: Wike Ya Bayyana Wanda Zai Marawa Baya
