Zaben Fidda Gwani a Jihar Adamawa Da Taraba

Sanata Emmanuel Ocheja, shugaban kwamitin zaben fidda gwani na jihar Taraba ya bayyana tsohon mukaddashin gwamnan jihar Taraban, Sanata Sani Danladi, wanda bai dade da komowa jam’iyar APC ba da cewa shi ya lashe zaben fidda gwani da kuri’u 6,609 daga cikin kuri’u 7,387 da aka kada.

An dai shafe fiye da kwana uku ana sabi-dora-ta, game da zaben fidda gwani na jihar wanda ‘yan takara goma suka shiga zaben, da suka hada da wani tsohon minista Joel Ikenya da ya zo na biyu da kuma tsohon mukaddashin gwamnan jihar Alhaji Garba Umar UTC, dake da kuri’u 5,504.

To sai dai kuma jim kadan da bayyana wannan sakamako, sai sauran ‘yan takarar da suka sha kaye suka ce ba zata sabu ba wai bindiga a ruwa, lamarin da ya kaisu garzayawa Abuja bisa zargin cewa ba a gudanar da zabe ba cikin adalci.

Kamar Taraba, a makwabciyarta ma wato jihar Adamawa yanzu ‘yan takarar kujerar Sanata ne ke barazanar garzayawa kotu biyo bayan bayyana sunan Sanata Binta Masi Garba, a matsayin ‘yar takara tilo daga mazabar Adamawa ta Arewa.

‘Yan takarar dai sun ce basu amince da wannan mataki na uwar jam’iyyar ba, inda mafi yawansu suka yi barazanar zuwa kotu domin a bi musu hakkinsu.

Wakilin Muryar Amurka yayi kokarin ji daga bakin shugabanin jam’iyyar a jihar, to amma kowa yayi gum, domin gudun ance kace, kuma wannan ma ko na zuwa ne yayin da ake haramar gudanar da zaben kato bayan kato na fidda gwani na gwamna ayau alhamis, inda gwamnan jihar Sanata Bindo Jibrilla zai fafata da tsohon shugaban hukumar EFCC Mallam Nuhu Ribadu da kuma Dakta Mahmud Halilu Ahmad dake zama kanin matar shugaban kasa.

More from this stream

Recomended