Zaben cike gurbin jihar Kogi: An kashe barayin akwatin zabe biyu

[ad_1]
Aƙalla mutane biyu aka kashe lokacin zaben cike gurbi na kujerar dan majalisar wakilai dake wakiltar mazabar Kogi/Lokoja.

A jiya Asabar ne Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta Ta Ƙasa wato INEC ta gudanar da zaben cike gurbi a mazabar.

Zaben da aka fara gudanar da shi cikin tsanaki da kwanciyar hankali inda aka samu fitowar jama’a sosai amma daga bisani rikici ya dabaibaye zaben.

Wasu mutane da ake zargin yan bangar siyasa ne sun rika bi tashohin zabe suna tayar da hankali tare da tafka magudin zaɓe.

William Aya, mai magana da yawun rundunar ƴansandan jihar Kogi ya ce an kashe wani mutum mai suna, Yadau Umoru a tashar zabe ta Unguwan Pawa dake kusa da Fadar Maigari lokacin da yake kokarin satar akwati.

Ya ce an ajiye gawar mamacin a cibiyar kula da lafiya ta tarayya dake Lokoja.

An kuma kashe wani mutum da ba a tantance waye shiba a tashar zabe da kusa da ofishin rarraba hasken wutar lantarki shiyar Abuja dake Lokoja lokacin da yake kokarin gudu da akwatin a zaɓe.

Aya ya ce har ya zuwa yanzu ba a iya gane mutumin ba.

Tuni jam’iyar PDP dama wasu jam’iyu suka yi kira da a soke zaben.
[ad_2]

More News

Wani dan ta’adda ya faɗa hannun ƴan sanda a Yobe

Rundunar ƴan sandan jihar Yobe ta sanar da kama Haruna Muhammad mai shekaru 40 wanda aka yi ittifakin cewa shi ne shugaban wasu gungun...

Wani mahajjacin Jihar Filato ya riga mu gidan gaskiya a Makka

Allah ya yi wa wani mahajjacin jihar Filato Ismaila Musa rasuwa a birnin Makka na kasar Saudiyya.Daiyabu Dauda, babban sakataren hukumar jin dadin alhazai...

NAFDAC ta ce kar ƴan Najeriya su riƙa cin abincin da ya wuce kwana 3 a firij

Darakta Janar ta Hukumar NAFDAC, Farfesa Moji Adeyeye, ta bukaci ‘yan Najeriya da su guji ajiye dafaffen abinci a cikin firiji sama da kwanaki...

Ƴanbindiga sun kashe mutane a Jihar Kaduna

An tabbatar da mutuwar mutane shida yayin da wasu da dama tare da yin garkuwa da su a lokacin da wasu ‘yan bindiga suka...