A cigaba da kokarin da Bola Ahmad Tinubu yake na ganin ya lashe tikitin takarar shugaban kasa a jam’iyar APC dama lashe babban zaben kasa na shekarar 2023 a ranar Laraba,ya gana da yan majalisar datttawa da suka fito daga jam’iyar APC.
Tinubu ya gana da su ne domin bayyana musu aniyarsa tare da neman goyon bayansu a takararar da yake yi.
Tsohon gwamnan na jihar Lagos ya fadawa sanatocin irin nagarta da kuma kwarewar da yake da ita da yakamata su yi la’akari da su wajen goya mishi baya.