Za’a Gina Tashar Motoci Ta Zamani A Obolo Afor Dake Jihar Enugu

[ad_1]

Tashar ta farko za’a ginata ne a garin Obollo-Afor dake jihar Enugu, inda tuni aka samu katafaren fili mai tsawon kadada 16, kuma zata dauki dukkan manyan motoci da kan tsaya a garuruwan dake kan manyan hanyoyin da hakan kan haddasa cunkoso da ma hatsari,.

Wakili a hukumar kula da wadannan tashoshi Injiniya K.C. Izuwah yace ya kamata gwamnatin Nigeria ta kafa duka a zata tilasta direbobi su rika tsayawa don hutawa; don an gano yawancin direbobin kan yi barcin sa’a 4 ne kacal cikin sa’o’I 24 inji Injiniya Chidi K.C. Izuwah.

Ya ci gaba da cewa akwai bukatar samar da tashoshin madakatar manyan motocin domin direbobi su samu su huta a kuma kaucewa hadarin da kan faru a kan hanyoyi sanadiyar ajiye manyan motocin a gefen tituna

Izuwah ya ce tashoshin na zamani za su zama da masaukan baki,gidajen abinci, bankuna, asibitoci, kotuna, wuraren ibada, makanikai har ma da wajen shakatawa da wanke motoci.

Shugaban hukumar zirga-zirgar harkar kasuwanci ta jiragen ruwa Hassan Bello, ya ce za a fara aikin nan take kuma za a kafa irin tashoshin a duk garuruwan da manyan motoci ke tsayawa, baya ga rage hatsaari, zai kuma bunkasa tattalin arzikin al’ummar yankunan.

Kungiyar direbobi da ake kira NURTW a takaice data masu manyan motocin sufuri wacce ake kira NARTO a takaice, sun amince da shiga wannan tsari don inganta rayuwar direbobin da kula da lafiyar motocin.

A saurari rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya

[ad_2]

More News

Shehin Musulunci ya nemi masu kuÉ—i da su raba wa talakawa naman Salla

Mataimakin Babban Limamin Masallacin Yobe da Cibiyar Musulunci, Malam Mohammad Ali Goni Kamsulum, ya yi kira ga masu hannu da shuni da su rika...

Ƴansandan sun yi artabu da ƴanbindiga a Abuja

Jami’an ‘yan sanda daga babban birnin tarayya Abuja sun kashe wani dan bindiga tare da cafke uku a wani samame da suka kai.Ƴan sandan...

An wallafa sunaye da hoton fursunonin da suka tsere daga gidan yarin Suleja

Hukumar NCoS dake lura da gidajen gyaran hali da tarbiyya ta fitar da sunaye da kuma hotuna na É—aurarrun da suka tsere da gidan...

An wallafa sunaye da hoton fursunonin da suka tsere daga gidan yarin Suleja

Hukumar NCoS dake lura da gidajen gyaran hali da tarbiyya ta fitar da sunaye da kuma hotuna na É—aurarrun da suka tsere da gidan...