Za mu yi wa Kwankwaso da Shekarau adalci a Kano – PDP

[ad_1]

Kwankwaso da Shekarau

Hakkin mallakar hoto
@KwankwasoRM

Kusan ana iya cewa Jam`iyyar adawa ta PDP a jihar Kano na kunshe da wasu manyan bangarorin siyasa uku, inda kowane gida ke tinkaho da jama`arsa.

Wadannan ‘yan siyasa sun hada da tsoffin gwamnonin jihar biyu, wato Rabi`u Musa Kwankwaso wanda ya yi wa jam`iyyar kome da Malam Ibrahim Shekarau da kuma tsohon minista, Aminu Wali ke jagoranta.

Duk da cewa sun hade a jam`iyya daya wato PDP, masana na cewa akidojin bangarorin sun banbanta da juna.

Sanata Mas`ud El-Jibrin Doguwa shi ne shugaban jam`iyyar PDP na jihar Kano.

A tattaunawarsa da BBC kan yanda yake ganin jagoranci da kuma zaman da bangarori ukun ke yi a jam`iyyar:

Ya ce ‘daman wadanda suka tafi yawon ba nisa suka yi da dakunansu ba, kuma ba mu sa kowa a dakin nasu ba, saboda mun san za su dawo domin ba tafiya ce mai dorewa ba.’

Sanatan ya kuma ce ‘dawowarsu a yanzu za ta taimaka masu wajen aiwatar da abin da ba a taba yin irin sa a siyasar Kano ba.

Babu dai wanda ya yi tsammanin cewa tsoffin gwamnonin biyu za su kulla kawance karkashin inuwar jam’iyya guda.

Sai dai a wannan lokaci da ake ganin cewa jam’iyyar PDP na kunshe da wasu manyan gidajen siyasa.

Wadanda duka suke da tasiri a zaben 2019, Sanata Mas’ud ya ce a matsayin sa na shugaba wanda kuma ake sa ran ya yi adalci, duk wanda ya tsaya takara a wadanan bangarori uku kuma jama’a suka nuna shi suke so, to shi za su bai wa takara.

Kowanne bangare dai na ganin akwai gagarumar gudunmawar da zai bai wa jam’iyyar ta kai ga nasara a zaben 2019.

Wannan dalili ya sa ake hasashen yiwuwar samun rabuwar kawunan.

Amma a cewar shugabannin PDP a matakin Jiha, duk wanda ya kawo wa jam’iyyar gudunmawar cin zaben zai samu abinda yake so.

Hakazalika su ma wadanda aka tarar a cikin jam’iyyar za a musu adalci.

“Muna kan tattaunawa, kuma har yanzu ba a kai ga matakin cewa kowanne bangare akwai kaso na musamman da za a ba shi a Jam’iyya ba” in ji sanata Mas’ud.

“Burin jam’iyyar adawa ta PDP a yanzu bai wuce samun hadin kai wurin aiki a matakin jiha da kasa ba, domin ganin an warware duk matsalolin jam’iyyar da na neman takara.”

[ad_2]

More News

Sakamakon NECOn 2024 ya fito

Hukumar shirya jarabawar ta kasa ta fitar da sakamakon jarabawar kammala sakandare ta watan Yuni/Yuli 2024, inda kashi 60.55 cikin 100 na waɗanda suka...

Ƴan Najeriya na shan baƙar wahala—Janar Abdulsalami

Tsohon shugaban kasa, Janar Abdulsalami Abubakar, ya ce wahalhalun da ake fama da su a Najeriya na kara tabarbarewa, kuma rabon kayan agajin ba...

EFCC ta musalta cewa Yahaya Bello na tsare a ofishin hukumar

Hukumar EFCC dake yaƙi da masu yiwa tattalin arzikin ƙasa ta'annati ta ce tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello baya ya tsare a hannunta. A...

Mutane 18 sun ƙone ƙurmus a wani hatsarin mota

Aƙalla fasinjoji 18 ne suka ƙone ƙurmus a wani hatsarin mota da ya faru akan babbar hanyar Ojebu-Ode zuwa Ore a yankin Ogbere dake...