Za mu yi da’a ga kotu a kan Sowore – Malami | BBC Hausa

Latsa hoton da ke sama don kallon cikakken bidiyon

Ministan shari’ar Najeriya Abubakar Malami ya ce gwamnatin kasar za ta yi da’a ga umarnin kotun kasar a kan sakin dan siyasa kuma dan gwagwarmaya, Omoyele Sowore, wanda yake hannun hukumomin kasar.

A farkon makon nan wata babbar kotun tarayya a Abuja da ke Najeriya ta bai wa hukumar tsaro ta farin kaya DSS umarnin sakin mawallafin jaridar Sahara Reporters ta intanet Omoyele Sowore.

Sai dai a yayin yanke hukuncin, kotun ta umarci Sowore ya bayar da fasfonsa na tafiye-tafiye.

Hakan na zawa ne bayan da DSS ta janye karar da ta kai babbar kotun tarayyar wanda ta nemi a ci gaba da tsare Omoyele Sowore kan zargin hannu a ta’addanci.

More from this stream

Recomended