Za Mu Karɓe Mulkin Najeriya a 2027, Sauya Sheƙa Ba Zai Lalata PDP Ba—Bala Mohammed

Gwamnan Jihar Bauchi kuma Shugaban Gwamnonin Jam’iyyar PDP, Bala Mohammed, ya bayyana tabbacin cewa jam’iyyar za ta dawo kan madafun iko a 2027 duk da sauya sheƙa da wasu manyan ‘ya’yan jam’iyyar ke yi zuwa jam’iyyar APC mai mulki.

Mohammed ya faɗi haka ne a ranar Asabar yayin da yake zantawa da manema labarai a birnin Abuja. Ya ce jam’iyyar tana aiki cikin nutsuwa domin ta daidaita tsarin cikin gida da kuma farfaɗo da amincewar al’umma gare ta.

Ya bayyana damuwarsa kan yadda wasu gwamnoni da ‘yan majalisa ke barin jam’iyyar zuwa APC, amma ya jaddada cewa ana ci gaba da ƙoƙari wajen ƙarfafa PDP.

Gwamnan ya zargi gwamnatin tarayya ta jam’iyyar APC da amfani da ƙarfin iko wajen raunana jam’iyyun adawa da nufin mayar da Najeriya ƙasa mai jam’iyya ɗaya.

Duk da haka, ya ce sauya sheƙar ba zai hana PDP samun nasara ba domin har yanzu tana da gagarumin goyon bayan talakawa.

More from this stream

Recomended