Za mu ci gaba da ƙalubalantar su Ganduje – Shekarau

Tsohon gwamnan Kanon ya kuma nuna rashin jin dadinsa da wasu kalmomin batanci da ta ce gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya yi amfani da su jim kadan bayan hukuncin kotu da ke cewa bangaren gwamnan ke da halastaccen shugaba.

A ranar Alhamis ne dai kotun daukaka kara ta tabbatar da shugabancin jam’iyyar ga Abdullahi Abbas, kuma sa’o’i da yanke wannan hukuncin uwar jam’iyya ta kasa ta mika masa takardar shaidar shugabanci, matakin da bai yi wa ɓangaren Shekarau dadi ba.

A tattaunawarsa da BBC Hausa, Sanata Ibrahim Shekarau ya ce uwar jam’iyya ta nuna rashin adalci kuma sun yi mamakin irin kalaman da suka fito daga bakin Gwamna Abdullahi Ganduje.

Umaymah Sani Abdulmimin ta fara ne da tabayar yadda suka ji da hukkunci. Ga yadda hirar ta kasance:

Shekarau: “Kamar yadda aka sani kowane ɗan adam idan bai samu yadda yake so ba zai ji babu daɗi, amma muna karɓar hukunci daga Allah kuma muna kyautata wa Allah zato ya zama alheri a gare mu.

“Mun saurari wannan hukunci kuma mun fara tattauna wa da lauyoyinmu.”

To mene ne mataki na gaba?

Shekarau: Mataki na gaba shi ne za mu ci gaba da bin haƙƙinmu kuma za mu bai wa lauyoyinmu umarnin bin sawun karɓo wannan hukunci kuma su tafi Kotun Koli. Za mu ɗaukaka ƙara.

“Kuma wani abu da ya fito fili ya nuna rashin adalci musamman daga shugabancin uwar jam’iyya shi ne ganin yau wata biyu muna da hukuncin Babbar Kotu a hannunmu cewa muke da jam’iyya.

“Muka ce wa jam’iyya a rantsar a bai wa shugabamnmu takardar shaidar, alabashi idan sakamakon Kotun Koli ya fito aka samu saɓani sai a canza, amma aka ce a’a mu haƙura a zo a yi maganar sulhu.

“Abin mamaki yau da aka aka yi wannan hukunci ba a cika awa biyu ba aka kira su aka bai wa ciyaman ɗinsu takarda cewa jam’iyya su ta sani a ciyaman.

Yaya kuke kallon uwar jam’iyya a yanzu?

Shekarau: “Ba ta yi mana adalci ba domin sanda muke da hukunci a hannu ta ƙi cewa muke da jam’iyya.

Kuma ɓangaren shari’a na jam’iyya na hedikwata sun yi rubutu sun bai wa shugaban jam’iyya na kasa shawarar cewa a ba mu shaidar cewa muke da jam’iyya a wannan lokaci har sai idan an samu hukunci sabanin wannan, aka ce a’a.

Tun da an bai wa ɓangaren Ganduje shaida, ba kwa ganin kamar komai ya zo ƙarshe?

“A’a ai hukunci kotun daukaka kara suka bi suka ba su, mu kuma za mu bi haƙƙinmu da kyau.

Za ku bar jam’iyyar ne idan Kotun Koli ta sake tabbatar da hukuncin Kotun Daukaka Kara?

“Babu zancen barin jam’iyya. Ai don ƴan jam’iyya muke wannan jayayyar. Kuma hukuncin zama ko fita daga jam’iyya ba na mutum daya ba ne.

Idan ba ku yi nasara ba a Kotun Koli za ku yi wa bangaren Ganduje mubaya’a?

Ai mu masu biyayya ne ga umarnin kotu. Shi ne ma abin da ya jawo muka ji ba daɗi da uwar jam’iyya ta nuna akwai ‘yar bora da ‘yar mowa.

Sannan na biyu, mu da muke da hukunci a hannu, ba mu zagi kowa ba, ba mu ci mutuncin kowa ba, idan an kira mu taro muna zuwa, amma yau ɗin nan ana fitowa kotu, duk duniya ta ji yadda mai girma gwamna bai riƙe girmansa ba ya yi kalmomi naɓatanci.

“Abin kunya ne ma akai ga haka, mun ɗauka jam’iyya za ta ja kunne, amma sai ma aka kira su aka ba su satifiket.

“Mu yanzu abin da muke cwa mutane su yi hakuri su saurare mu muna nan za mu ci gaba da bin hakkin yan jam’iyya.”

More from this stream

Recomended