Za a yanke wa wata mata hukuncin kisa a Saudiyya

[ad_1]

Israa al-Ghomgham's supporters released a photograph showing her as a young girl

Hakkin mallakar hoto
Twitter/@IsraaAlGhomgham

Image caption

Magoya bayan Israa al-Ghomgham sun fito da hotonta lokacin tana yarinya

Rahotanni sun ce masu shigar da kara a Saudiyya sun bukaci a yanke hukuncin kisa ka masu fafutika biyar, cikin su har da mai fafutikar kare hakkin mata Israa al-Ghomgham.

Kungiyar kare hakkin dan adam ta Human Rights Watch ta ce a kwanakin baya ne wata kotun da ke yanke hukunci kan ayyukan ta’addanci ta tuhume su da laifin shiga zanga-zanga a yankin Qatif.

Galibin mazauna yankin ‘yan Shia ne marasa rinjaye kuma ya yi kaurin suna wajen yawaita gudanar da zanga-zanga.

An yi amannar cewa Ms Ghomgham ita ce ‘yar kasar Saudiyya ta farko da take fuskanat hukuncin kisa saboda ayyukanta na kare hakkin mata.

Human Rights Watch ta yi gargadin cewa hukuncin da aka yanke mata “zai haifar da mummunan sakamako ga sauran masu rajin kare hakkin mata da ke daure a gian yari.” kasar.

Mahukuntan kasar ta Saudiyya sun daure akalla masu kare hakkin dan adam da na mata 13 tun daga tsakiyar watan Mayu, inda ake zargin su da yin ayyukan da ke barazana ga tsaron kasa. An saki wasu daga cikin su ko da yake har yanzu wasu na tsare ba tare da an tuhume su ba.

Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Human Rights Watch ta ce hukuncin babbar barazana ce ga masu fafutikar da ke daure

Human Rights Watch ta ce Ms Ghomgham mai fafutika ce da ta yi fice kan shigea gaba a zanga-zanga da ke faruwa a Qatif tun 2011.

‘Yan Shia sun sha yin bore domin matsa lamba kan musgunawar da gwamnatin ‘yan Sunna ke yi musu.

Rahotanni sun ce an tsare Ms Ghomgham da mijinta ne a watan Disambar 2015, kuma tun a wancan lokacin ake tsare da su a gidan kurkukun da ke Dammam.

[ad_2]

More News

Kwankwaso ya bada tallafin miliyan ₦50 ga mutanen da ambaliyar Borno ta shafa

Tsohon gwamnan jihar Kano kuma jagoran jam'iyar NNPP, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya bada tallafin naira miliyan 50 ga mutanen da ambaliyar ruwa a...

Sakamakon NECOn 2024 ya fito

Hukumar shirya jarabawar ta kasa ta fitar da sakamakon jarabawar kammala sakandare ta watan Yuni/Yuli 2024, inda kashi 60.55 cikin 100 na waÉ—anda suka...

Ƴan Najeriya na shan baƙar wahala—Janar Abdulsalami

Tsohon shugaban kasa, Janar Abdulsalami Abubakar, ya ce wahalhalun da ake fama da su a Najeriya na kara tabarbarewa, kuma rabon kayan agajin ba...

EFCC ta musalta cewa Yahaya Bello na tsare a ofishin hukumar

Hukumar EFCC dake yaƙi da masu yiwa tattalin arzikin ƙasa ta'annati ta ce tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello baya ya tsare a hannunta. A...