
Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar ya ce shi da wasu ƴan adawa za su samar da wata haɗaka ta jam’iyyu da za ta ƙwace mulki daga jam’iyar APC a zaɓen 2027.
Atiku ya bayyana haka ne a Abuja a ranar Alhamis a wurin wani taron ƴan jarida da wasu masu ruwa da tsaki kan sha’anin siyasa a Najeriya suka gudanar kan dokar ta ɓaci da shugaban ƙasa, Bola Ahmad Tinubu ya sanya a jihar Ribas.
Taron manema labaran ya samu halartar tsohon gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasiru El-Rufai, Emeka Ihedioha tsohon gwamnan jihar Imo, Salihu Lukman tsohon mamba a shugabancin jam’iyyar APC na ƙasa da kuma Babachir Lawal tsohon sakataren gwamnatin tarayya da sauran wasu da dama.
Da aka tambaye shi ko ƴan jam’iyun adawa suna ƙoƙarin samar da wata haɗaka da zata kalubalanci jam’iya mai mulki Atiku ya amsa eh haka ne.
Ya yi allawadai da matakin da Tinubu ya ɗauka a Ribas inda ya ce shugaban ya fifita san rai wajen ayyana dokar tabacin.