Za a gudanar zaɓen ƙananan hukumomin Jihar Ribas a ranar 9 ga Agusta

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Jihar Ribas (RSIEC) ta bayyana ranar 9 ga Agusta, 2025, a matsayin ranar da za a gudanar da sabon zaɓen shugabannin ƙananan hukumomi a jihar.

Shugaban hukumar, Mai Shari’a (ritaya) Adolphus Enebeli, ya bayyana hakan ne yayin wani taron tattaunawa da masu ruwa da tsaki, tare da ƙaddamar da jadawali da ƙa’idojin zaɓen na shekarar 2025, a hedikwatar RSIEC da ke titin Aba a birnin Fatakwal, ranar Laraba.

Da yake jawabi ga mahalarta taron, Mai Shari’a Enebeli ya tabbatar da aniyar hukumar wajen gudanar da zaɓe mai inganci, gaskiya, da adalci, tare da kira ga jam’iyyun siyasa da su kiyaye dokoki da ƙa’idojin da aka gindaya.

More from this stream

Recomended