Gwamnan jihar Adamawa, Ahmad Fintiri ya amince a fara biyan mafi ƙarancin albashi na naira N70,000 ga ma’aikatan jihar da kuma na ƙananan hukumomi.
Shugaban ƙungiyar ƙwadago ta NLC reshen jihar, Kwamared Emmanuel Fashe shi ne ya bayyana haka ga manema labarai bayan fitowarsa daga wata ganawar sirri da suka yi da gwamnan a ranar Talata.
A cewar sa ma’aikatan gwamnatin jihar za su fara karɓar sabon ƙarin albashin daga watan Agusta a yayin da takwaransu na ƙananan hukumomi za su fara karɓar sabon ƙarin daga watan Satumba.
Kwamared Fashe ya ƙara bayyana cewa za ayi amfani da tsarin ƙarin albashi da aka yi amfani da shi a shekarar 2019 kafin hukumar kayyade albashi ta ƙasa ta fitar da sabon tsari da za ayi da shi amfani da shi a yanzu.
Ya ce gwamna ya bada muhimmanci ga walwalar ma’aikata shi ya sa ya gaggauta aiwatar da sabon tsarin albashi.