Gwamnatin Jihar Kano ta rattaba hannu kan wata yarjejeniya da kamfanin Kodong Manufacturing Nigeria Limited daga ƙasar China, wanda zai riƙa haɗa motoci da babura masu amfani da batir, tare da samar da wuraren cajinsu a fadin jihar.
A yayin bikin sanya hannun yarjejeniyar da aka gudanar a harabar kamfanin dake garin Dansudu, karamar hukumar Tofa, Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo, ya jaddada aniyar gwamnatin jihar na ci gaba da samar da yanayi mai kyau don jan hankalin masu zuba jari.
Ya kuma bayyana cewa gwamnatin Injiniya Abba Kabir Yusuf ta cire duk wani shinge daga ɓangaren gwamnati da ke kawo cikas ga harkokin kasuwanci a jihar, domin bunkasa tattalin arziki.