
Ƙasar Amurika ta tattara sunayen mutane 201 ƴan Najeriya waɗanda za a taso ƙeyarsu ya zuwa gida a cigaba da yakin da shugaban kasar, Donald Trump ke yi da bakin haure dake zaune ba bisa ka’ida ba a ƙasar.
Bianca Odumegwu Ojukwu ƙaramar ministar harkokin waje ta Najeriya ce ta bayyana haka lokacin da jakadan Amurka a Najeriya, Richard Mills ya kai mata ziyara a Abuja.
Mills ya ce ” Waɗanda za a dawo su ɗin za a sauke su a Lagos babu yiyuwar a sauke su a Fatakwal ko Abuja,”
“Rukunin farko za su kasance fursunoni waɗanda suka aikata laifi aka yanke musu hukunci suke zaman gidan yari,”
“Wasu daga cikinsu sun karya dokokin shiga da fice na Amurka. Sun ɗaukaka ƙara amma ba su yi nasara ba amma duk da haka sun cigaba da zama a Amurka,”
A cewar wata sanarwa da aka fitar ranar Lahadi, Magnus Eze mai magana da yawun ministar ya ce dukkanin jami’an biyu sun warware batun duk wata damuwa da ake da ita kan batun kwaso mutanen inda Ojukwu ta nemi da a dawo su cikin mutunci da girmamawa.