
Baƙin haure aƙalla miliyan biyu hukumar dake lura da shige da fice ta Amurka ta tabbatar cewa za a tasa keyarsu ya zuwa ƙasashen da suka fito.
Tasa keyar mutanen na zuwa ne dai-dai lokacin da shugaban ƙasar Amurika, Donald Trump ke cigaba da tabbatar da yakin da yake da bakin haure a kasar.
Hukumar ta ce akwai sunayen mutane 1,445,549 dake cikin jerin sunayen da hukumar ta tantance domin mayar da su gida.
A cikin wannan adadi akwai yan Najeriya 3690 wanda hakan ya sa ta zama ƙasa ta biyu a Nahiyar Afirka inda take bin ƙasar Somalia da ke da mutane 4,090.
Ƙasar Ghana ce ta kasance a mataki na uku da mutane 3,228.
Tuni dai gwamnatin ƙasar, Amurka ta shawarci ƙasashen da abun ya shafa da su karɓi ƴan kasar ta su da aka dawo da su gida.