Ranar Lahadi za a kara tsakanin Barcelona da Real Madrid a wasan hamayya na farko a bana da ake kira El Clasico a gasar La Liga.
Real Madrid ce za ta fara ziyartar Barcelona a wasan mako na 10 a babbar gasar ta Sifaniya da za su kece raini a Camp Nou.
Karon farko kenan da Barcelona wadda take ta bakwai a teburin La Liga za ta buga El Clasico ba tare da Lionel Messi ba, tsohon kyaftin din kungiyar.
Haka itama Real Madrid za ta buga wasan a karon farko ba tare da tsohon kyaftin dinta ba Sergio Ramos, wanda ya buga El Clasico 45 iri daya da yawan wanda Messi ya yi wa Barcelona.
Dukkan yan wasan biyu sun koma taka leda a Paris St Germain a bana, bayan da Real ba ta tsawaita kwantiragin Ramos ba, ita kuwa Barcelona ta fada matsin tattalin arziki da ta kasa biyan albashin Messi koda ta gabatar masa da kunshin kwantiragi.
Messi dai ya fara buga El Clasico ranar 19 ga watan Nuwambar 2005, inda Barcelona ta doke Real Madrid 3-0 karkashin jagorancin Ronaldinho.
Messi shine kan gaba a cin kwallaye a wasan na hamayya mai guda 26 a raga, kuma shine na daya a yawan bayar da kwallo aka zura a raga har guda 14.
Kungiyoyin biyu sun fara karawa ranar 13 ga watan Mayun 1902 a Copa de la Coronacion inda Barcelona ta yi nasara a kan Real Madrid da ci 3-1, sun kuma buga a bayan nan ranar 10 ga watan Afirilun 2021, inda Real Madrid ta yi nasara da ci 2-1 a La Liga.
Wasannin mako na 10 a gasar La Liga:
Ranar Juma’a 22 ga watan Disamba
Ranar Asabar 23 ga watan Oktoba
- Valencia da Real Mallorca
- Cadiz da Deportivo Alaves
- Elche da Espanyol
- Athletic Bilbao da Villarreal
Ranar Lahadi 24 ga watan Oktoba
- Sevilla da LevanteMatch details
- FC Barcelona da Real Madrid
- Real Betis da Rayo Vallecano
- Atletico Madrid da Real Sociedad
Ranar Litinin 25 ga watan Oktoba