Za a Bude Makarantu Ga Dalibai a Najeriya Domin Yin Jarrabawar WAEC

Gwamnatin Najeriya ta bayyana cewa za a bude makarantu a ranar 4 ga watan Augusta ga daliban da ke ajin karshe a makarantun Sakandare domin rubuta jarrabawar WAEC.

Gwamnatin ta bayyana matakin ne a cikin watan sanarwar da ma’aikatar ilimi ta fitar a yau Litinin wacce ke dauke da sa hannun daraktan yada labarai na Ma’aikatar, Ben Bem Goong.

Wannan matakin ya biyo bayan shafe sa’o’i ana tattaunawa a yau tsakanin ma’aikatar ta ilimi da kwamishinonin ilimi da kuma masu ruwa da tsaki a harkokin ilimi a kasar.

Sanarwar ta bayyana yadda aka umarci ‘yan ajin karshe da su koma makaranta da an kammala bikin sallah mai zuwa domin shirin yin jarrabawar wacce za a fara a ranar 17 ga watan Augusta.

A tattaunawar tasu, an Kuma bayyana cewa makarantu za su bukaci taimako daga gwamnatin tarayya wajen iya budewa cikin gaggawa.

Makarantu a kasar daga matakin farko zuwa karshe sun shafe watanni a garkame saboda kokarin takaita yaduwar cutar Coronavirus.

A cikin makonnin da suka gabata gwamnatin ta bayyana cewa ba za a gudanar da jarrabawar WAEC ba saboda cutar, amma yanzu gwamnatin ta sauya matsayarta.

More News

Yawan Mutanen Da Suka Mutu A Wutar Da Wani Matashi Ya Cinnawa Wani Masallaci A Kano Sun  Karu Zuwa 16

Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta ce yawan mutanen da suka mutu sakamakon wutar da wani ya cinnawa wani masallaci a ƙauyen Gadan a...

An fara rushe wasu gine-gine 500 a kasuwar Karmo dake Abuja

Hukumar FCTA dake kula da birnin tarayya Abuja ta fara rushe gine-gine sama da 500 da aka yi ba bisa ka'ida ba a kasuwar...

Tinubu ya tarbi shugaban kasar Senegal Bassirou Faye a fadar Aso Rock Villa

A ranar Alhamis ne shugaba Bola Tinubu ya tarbi shugaban kasar Senegal Bassirou Faye a fadar Aso Rock Villa, a ziyarar da Faye ya...

NEMA ta karɓi ƴan Najeriya 150 da aka dawo dasu gida daga ƙasar Chad

Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Ƙasa NEMA ta ce ta karɓi ƴan Najeriya 150 da aka dawo da su bayan da su ka maƙale...