Mambobin kwamitin sulhu da kuma wasu jiga-jigan jam’iyar APC daga jihar Adamawa sun gana da shugaban jam’iyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje ranar Juma’a a hedkwatar jam’iyar dake Abuja.
Tawagar ƙarƙashin jagorancin Sanata Mohammed Mana sun gana da Ganduje ne domin sake duba shirye-shiryen su da kuma tsare-tsare gabanin zaɓen gwamnan jihar na shekarar 2027.
Idan za a iya tunawa jam’iyar APC a jihar Adamawa ta shiga cikin rikici gabanin zaɓen gwamnan jihar na 2023 abun da ya jawo jam’iyar ta sha kayi a zaɓen a hannun jam’iyar PDP.
Da ya ke jawabi ga ƴan jaridu bayan ganawar sirrin shugaban kwamitin sulhun, Sanata Mana ya ce Ganduje ya ɗora musu alhakin aikin haɗa kan ƴan jam’iyar gabanin zaɓen.
“Adamawa jiha ce mai muhimmanci kuma zamu mayar da hankali wajen tabbatar da APC ta lashe kujeru mafiya yawa a 2027,” ya ce.
“Zamu tuntubi waɗanda suke jin anyi watsi da su a lokacin zaɓen fidda gwani da kuma zaɓen gama gari domin hada kan jam’iyar karkashin tutar APC.”
A jawabin ta Sanata Binta Masi Garba ta bayyana kwarin gwiwar da take da shi kan ƙokarin kwamitin inda ta ce da ikon Allah jam’iyar za ta samu nasara a zaɓen.