
Hukumar Zaɓe mai Zaman Kanta ta Najeriya ta ce tana shirye-shiryen ɗaukaka ƙara kan hukuncin kotu wanda ya bai wa waɗanda suka shigar da ƙara damar yin zaɓe da katin zaɓe na wucin-gadi.
A wata sanarwa da hukumar ta wallafa a shafinta na tuwita, INEC ta ce “an kai mata hukuncin da babbar kotun tarayya da ke Abuja ta yanke, wanda ya bai wa waɗanda suka shigar da ƙarar damar yin amfani da katin zaɓensu na wucin-gadi wajen kaɗa ƙuri’a.”
Bayanin ya ƙara da cewa “Hukumar na duba matakan da suka kamata ta wajen ɗaukaka ƙara domin ƙalubalantar hukuncin.”
A ranar Alhamis ne mai shari’a Obiora Egwuatu ya bai wa masu shigar da ƙarar gaskiya, inda ya ce suna da ƴancin amfani da katunansu na wucin-gadi domin kaɗa ƙuri’a.
Mai shari’ar ya ce kotu ta yanke hukuncin bisa dogaro da cewa hukumar zaɓen na da bayanan mutanen, kasancewar sun riga sun yi rajistar katin zaɓe.
Ita dai INEC ta ce babu wanda zai kaɗa ƙuri’a har sai ya gabatar da katin zaɓensa na dindindin, tare da sharaɗin cewa an iya tantance shi ta hanyar na’aur
INEC ɗin dai na fuskantar shari’o’i da dama tun bayan kammala zaɓen shugaban ƙasa na 25 ga watan Fabarairu.
A ranar Laraba ne hukumar zaɓen ta ɗage zaɓen gwamnonin jihohi da aka shirya gudanarwa ranar 11 ga watan Maris, bayan hukuncin da kotu ta yanke na ba ta umurnin sauya bayanan da ke cikin na’urar tantance masu kaɗa ƙuri’a ta BVAS.
Tun farko jam’iyyun adawa waɗanda ba su amince da sakamakon zaɓen shugaban ƙasa ba, musamman PDP da LP sun garzaya kotu domin samun izinin yin bincike a kan nau’urorin.
PDP da LP dai sun yi zargin an tafka maguɗi, bayan da hukumar ta gaza tura sakamakon zaɓen ta na’ura daga rumfunan kaɗa ƙuri’a.