Yunwa da ƙishirwa na yi wa ƙananan yara barazana a Gaza

A yayin da Isra’ila ke ci gaba da kai munanan hare-hare a Gaza, ƙananan yara na cikin wadanda abin ya fi shafa.

Baya ga haka rashin ruwan sha da abinci na ci gaba da yin barazana.

“Abin da muke gani a Gaza a yanzu shi ne kisan gillar da ake yi wa kananan yara a hankali,” in ji Alexandra Saieh, shugabar manufofin agaji da bayar da shawarwari a kungiyar Save the Children International.

Ma’aikatar lafiya ta Gaza ta ce yara shida ne suka mutu a arewacin Gaza sakamakon rashin ruwa da rashin abinci mai gina jiki a asibitocin Kamal Adwan da al-Shifa, yayin da wasu ke cikin mawuyacin hali.

More from this stream

Recomended