Yohanna ya karɓi rantsuwar kama aiki bayan da ya maye gurbin sanata Abbo a majalisar dattawa

Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau I Jibrin ya rantsar da Amos Yohanna a matsayin sabon sanatan da zai wakilci mazabar Arewacin Adamawa.

An rantsar da shi a zaman majalisar na ranar Laraba da Barau ya jagoranta.

Yohanna ya maye gurbin Elisha Abbo wanda kotun daukaka kararrakin zabe ta soke zaɓensa a ranar Litinin da ta gabata.

Kotun daukaka karar dake Abuja ta soke nasarar zaɓen da Abbo ya samu a ƙarkashin jam’iyar APC.

Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta kasa INEC ce ta ayyana Abbo a matsayin wanda ya lashe zaɓen ranar 25 ga watan Faburairu 2023 amma Yohanna ya yi watsi da sakamakon inda ya tafi kotu.

More from this stream

Recomended