Yawan mutanen da suka mutu a hatsarin kwale-kwalen jihar Niger ya kai 42

Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta jihar Niger NSEMA ta ce yawan mutanen da suka mutu a hatsarin kwale-kwale da ya faru a jihar sun kai mutum 42.

A ranar 1 ga watan Oktoba ne jirgin kwale-kwalen dake ɗauke da mutane sama da 300 akan hanyarsu ta zuwa wurin Maulidi  ya kife dasu a Gbajibo dake ƙaramar hukumar Mokwa ta jihar.

Tun bayar faruwar lamarin ne hukumar ta NSEMA da wasu sauran hukumomin bada agajin gaggawa suka duƙufa aikin ceto inda suka samu nasarar ceto sama da mutane 150.

Ibrahim Hussaini mai magana da yawun hukumar ta NSEMA ya ce an samu gano ƙarin gawarwaki shida da safiyar ranar Juma’a.

“Daga ƙarfe 6 na yammacin jiya zuwa 10 na safiyar yau ƙarin gawarwaki 6 aka gano hakan ya sa jimilllar gawarwakin ya kai 42,” ya ce

A ranar Alhamis ne shugaban ƙasa Bola Ahmad ya bawa hukumar dake lura da ruwayen Najeriya da ta binciko dalilin da yasa ake yawan samun yawan faruwar hatsarin kwale-kwale a jihar.

More from this stream

Recomended