Ranar Litinin din nan ce ranar da hukumomin ƙasar Saudiyya suka tsayar mastayin ranar cikar waadin kammala jigilar maniyyata aikin Hajjin bana daga kowace kusurwa ta duniya.
Da karfe 12 na tsakar daren yau Litinin agogon Saudiyya ne hukumomin na Saudiyya suka ce za su rufe filayen jiragen saman ƙasar 6 ga saukar duk wani jirgin da ya dauko maniyyata daga kowace kasa ta duniya.
Hakan ya sa ƙasashe musamman waɗan da ke da adadi mafi yawa na maniyyatan da ke rige-rigen ganin sun kammala jigilar maniyyatansu kafin cikar wa’adin.
Filayen jiragen su ne waɗan da aka keɓe domin jigilar maniyyatan na bana da ke biranen Riyadh, da Jiddah, da Madina, da Dammam, da Taif, da kuma Yanbu’u.