Yau ake hawan Arfa a kasa mai tsarki

[ad_1]

Filin Arfa

Image caption

Alhazai na amfani dalema dan kare rana

Sama da musulmai miliyan biyu ne daga sassa daban-daban na duniya suka fara aikin Hajjin bana a jiya lahadi.

An dai fara zaman Muna a ranar asabar din wanda wani bangare ne na cikamakin aikin hajji da kowanne musulmi zai aikata kafin ya samu cikakkiyar ibadar aikin hajjin.

A yau Litinin kuma dukkan maniyata za ta dunfari filin Arfa, inda za su shafe ranar ta yau su na gudanar da ibada da neman gafara ga Allah SWA.

Wadanda suke da iko da koshin lafiyar hawa dutsen Arfa kan yi kokarin aikata hakan dan koyi ga fiyayyaen halitta Annabi Muhammad SAW.

Anan filin Arfa musulmai za su sallaci Azahar da La’asar a matsayin Kasaru, sanna a ci gaba da ibada da zikiri da karatun Al-Kur’ani da Zikiri da gabatar da Sallah dan neman amincewar Allah SAW da dacewa a wannan rana.

Bayanai sun ce mahukuntan Saudiyya sun kara daukar matakai don tabbatar da ganin aikin hajjin ya gudana cikin nasara da kuma kauce wa matsalolin da aka fuskanta a baya.

Daga cikin tsare-tsare da aikace-aikace da dama da aka yi har da kirkiro wata sabuwar manhaja da za ta taimakawa Alhazai da suka bata.

[ad_2]

More News

Ƴansanda sun kama muggan ƴan fashi da makami

Jami’an hukumar ‘yan sanda reshen Elemoro reshen jihar Legas sun kama wasu mutane uku da ake zargi da hannu a fashi da makami a...

An kama wasu mutane biyu da hodar ibilis a Lagos

Rundunar ƴan sandan jihar Lagos ta sanar da kama wasu mutane biyu da aka samu ɗauke da ƙunshin hodar ibilis mai yawan gaske. Mai magana...

Ƴan sanda sun kama wani mutum ɗauke da bindigogi 20 a Kaduna

Rundunar Æ´an sandan jihar Kaduna ta ce jami'anta sun kama wani  riÆ™aƙƙen mai safarar bindiga inda aka same shi da bindigogin AK-47 Æ™irar gida...

Kwankwaso ya bada tallafin miliyan ₦50 ga mutanen da ambaliyar Borno ta shafa

Tsohon gwamnan jihar Kano kuma jagoran jam'iyar NNPP, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya bada tallafin naira miliyan 50 ga mutanen da ambaliyar ruwa a...