Yau ake bude makarantu a wasu jihohin Najeriya

Dalibai a aji

Bayan kwashe sama da wata shida sakamakon cutar korona, wasu jihohin Najeriya za su buÉ—e azuzuwa a yau don ci gaba da karatu.

Jihohin Kebbi da Kwara da kuma Katsina,na daga cikin jihohin da zasu bude makarantun a yau don ci gaba da karatu.

Za a bude makarantun firamare da sakandire na gwamnati da kuma masu zaman kansu ne cikin tsauraran matakan kariya saboda cutar korona.

Kwamishinan ilimi na jihar Katsina, Dakta Badamasi Lawal, ya shaida wa BBC cewa, an yi feshin kashe kwayoyin cututtuka a makarantu, sannan an tanadi wuraren wanke hannu, sannan kuma dole ne dalibai da malamai su rinka sanya takunkumin fuska.

Kwamishinan ya ce, an kuma raba zuwan dalibai makaranta, inda wasu zasu rinka zuwa da safe wasu kuma da yamma saboda ana so a rinka bayar tazara a tsakanin dalibai a kowanne aji.

Tuni dai kungiyar iyayen yara da malamai ta jihar Katsinan ta nuna farin cikinta game da komawar daliban makaranta.

Shi ma kwamishinan ilimi na jihar Kebbi Alhaji Muhammadu Magawatan Aleiro, ya shaida wa BBC cewa, suma sun dauki matakan kariya daga cutar korona ciki har da sanya takunkumi da kuma abin wanke hannu.

A nasu bangaren, daliban wadannan jihohi da zasu koma karatu a yau Litinin 5 ga watan Oktoba, sun bayyana farin cikinsu game da komawar ta su, inda wasu daga cikinsu ke cewa komawar tasu zata rage musu zaman banza.

A ranar Jumma’ar data gabata ne gwamnatin Najeriya ta bayar da sanarwar cewa za a bude makarantun daga ranar 12 ga watan Oktoban, 2020 bayan shafe sama da wata shida da rufe makarantun saboda bullar cutar korona.

Watanni shida da suka gabata ne hukumomi a Najeriya suka rufe makarantu a dukkanin fadin kasar saboda fargabar yaduwar annobar korona.

More News

Mai magana da yawun Tinubu ya ajiye aikinsa na wani lokaci

Mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai Ajuri Ngelale ya ajiye aikinsa na wani lokaci domin tunkarar matsalar lafiya.Mista Ngelale...

Ali Jita ya koma jam’iyar APC daga NNPP

Mataimakin shugaban majalisar dattawa dattawa, Sanata Barau Jibrin ya karɓi fitaccen mawakin Kannywood, Aliyu Isa Jita daga jam'iyar NNPP ya zuwa jam'iyar APC. Ali Jita...

An yi jana’izar mutumin da ya Æ™irÆ™iri tutar Najeriya

Iyalan marigayi, Pa Taiwo Akinkumi mutumin da ya ƙirƙiro tutar Najeriya sun yi bikin binne shi bayan da gwamnatin tarayya ta gaza cika alƙawarin...

‘Za a Æ™ara wa Æ´an bautar Æ™asa na NYSC alawus’

Babban daraktan hukumar yi wa kasa hidima ta kasa (NYSC) Birgediya Janar Yushau Ahmed, ya tabbatar wa ‘yan bautar kasar cewa za a kara...