Yaro Ɗan Shekaru Biyu Ya Mutu Bayan Fadawa A Cikin Rijiya A Kano

Wani mummunan al’amari ya faru a Jihar Kano, inda wani yaro mai suna Sa’idu Ahmad, mai shekaru biyu, ya rasu bayan ya fadi cikin rijiya a garin Kwankwaso da ke Karamar Hukumar Madobi.

Jami’in hulda da jama’a na Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano, Alhaji Saminu Abdullahi, ya tabbatar da faruwar lamarin a cikin wata sanarwa da ya fitar a Kano. Ya bayyana cewa lamarin ya faru ne da rana a ranar Laraba.

A cewarsa, hukumar ta samu kiran gaggawa daga Mataimakin Daraktan hukumar, Rabiu Garba, da misalin karfe 12:15 na rana. Ya ce an sanar da su cewa wani yaro ya fadi cikin rijiya, lamarin da ya sa nan take suka tura jami’an ceto zuwa wurin.

Abdullahi ya ce an ceto yaron a cikin halin suma, sannan daga bisani aka mika shi ga Umar Shehu na Sashen ‘Yan Sanda na Madobi. Ya kara da cewa ana gudanar da bincike domin gano musabbabin faruwar lamarin.

More from this stream

Recomended