‘ Yara kusan rabin miliyan za su mutu a bana ‘

Save the Children ta ce yunwa na galabaitar da yara a yankunan da ake yaki


Save the Children ta ce yunwa na galabaitar da yara a yankunan da ake yaki

Kungiyar agaji ta Save the Children ta kiyasta cewa yara sama da rabin miliyan da shekarunsu ba su haura biyar ba, za su mutu a wannan shekarar saboda tsananin yunwa a kasashe da yaki ya kassara.

Kungiyar ta ce bangarorin da ke rikici da juna na datse hanyoyin bada taimakon agaji da gangan.

Save the Children, ta ce alkaluman Majalisar Dinkin Duniya sun nuna cewa akwai yara sama a 1400 da suka fada cikin wannan yanayin a bara, bayan hana shigar da kayayakin jin-kai yankunan da ake rikici.

Karuwar alkaluman a cewar kungiyar ya biyo bayan rikicin Sudan ta Kudu da Yemen da Mali da kuma Syria.

Shugaban kungiyar Kevin Watkins ya ce amfani da yunwa a matsayin makamin yaki na neman zama ruwan dare

.

More News

Ƴansanda sun kama muggan ƴan fashi da makami

Jami’an hukumar ‘yan sanda reshen Elemoro reshen jihar Legas sun kama wasu mutane uku da ake zargi da hannu a fashi da makami a...

An kama wasu mutane biyu da hodar ibilis a Lagos

Rundunar ƴan sandan jihar Lagos ta sanar da kama wasu mutane biyu da aka samu ɗauke da ƙunshin hodar ibilis mai yawan gaske. Mai magana...

Ƴan sanda sun kama wani mutum ɗauke da bindigogi 20 a Kaduna

Rundunar Æ´an sandan jihar Kaduna ta ce jami'anta sun kama wani  riÆ™aƙƙen mai safarar bindiga inda aka same shi da bindigogin AK-47 Æ™irar gida...

Kwankwaso ya bada tallafin miliyan ₦50 ga mutanen da ambaliyar Borno ta shafa

Tsohon gwamnan jihar Kano kuma jagoran jam'iyar NNPP, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya bada tallafin naira miliyan 50 ga mutanen da ambaliyar ruwa a...