YANZU-YANZU: ‘Yan Bindiga Sun Kai Hari A Neja, Mutane Sama Da 30 Sun Rasa Rayukansu

Akalla mutane 30 ake fargabar sun rasa rayukansu, yayin da wasu da dama suka shiga hannun ‘yan bindiga, bayan wani mummunan hari da aka kai a wani yankin Jihar Neja.

Rahotanni sun bayyana cewa ‘yan bindigar, da ake zargin suna fitowa ne daga dajin Kainji Lake National Park, sun kai hari kasuwar wani ƙauye a Gundumar Kabe, Ƙaramar Hukumar Borgu, inda suka banka wa kasuwar wuta.

Maharan sun ƙona kasuwar tare da wawure kayan abinci da sauran kayayyaki, sannan suka rika harbin mazauna ƙauyen tare da yin awon gaba da wasu mutane a hanyoyin da ke kaiwa cikin dajin Kainji.

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, Wasiu Abiodun, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce tawagar tsaro ta haɗin gwiwa ta ziyarci wurin da abin ya faru, kuma ana ci gaba da ƙoƙarin ceto mutanen da aka sace.

A cewarsa, “Fiye da mutane 30 sun rasa rayukansu yayin harin, yayin da aka sace wasu mutane.”

More from this stream

Recomended