Rundunar ‘yan sandan jihar Kebbi ta sanar da tsare wasu jami’anta uku bisa zarginsu da hannu a kisan wani da ake zargi da sata a garin Jega.
Mai magana da yawun rundunar, CSP Nafi’u Abubakar, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar a Birnin Kebbi.
A cewar sanarwar, lamarin ya samo asali ne daga rahoton satar tayoyin babbar mota da wani ya kai ofishin ‘yan sanda na Division a Jega.
CSP Abubakar ya jaddada cewa rundunar tana jajirce wajen tabbatar da bin ka’idoji da dabi’un aikin dan sanda.
‘Yansanda Sun Tsare Jami’ansu Uku Bisa Zargin Kisan Wani Da Ake Zargi Da Sata a Jihar Kebbi
