Shugaba Muhammadu Buhari
Photo: Bashir Ahmad Twitter (Twitter)
Buhari ya yi wannan kira ne, kwana biyu, bayan da rahotanni suka nuna cewa, reshen kungiyar IS da ke yammcin Afirka na ISWAP, ya kashe wasu Kiristoci hade da wasu Musulmi.
“Na yi matukar bakin ciki tare da kaduwa bisa kashe mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba, wadanda mutane marasa tausayi da rashin imani suka rike su, suke kuma bata sunan addinin Islama” a cewar wata sanarwa da kakakin shugaba Buhari, Garba Shehu ya fitar a yau Juma’a.
Sanarwar ta kara da cewa, “kada mu bari a yi amfani da wata kafa, ‘yan ta’adda su gwara kanmu – ta hanyar hada Kiristoci da Musulmi fada, saboda wadannan mutane marasa imani ba wakilan addini Islama ba ne kuma ba jakadun miliyoyin Musulmi da ke sauran sassan duniya ba ne.”
A cewar Shugaba Buhari, “babu wani Musulmin kwarai, da zai rika ambatar “Allahu Akbar” yayin da yake kashe mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba, domin Al Qur’ani mai girma, ya sha yin Allah wadai da masu aikata hakan.”