‘Yan sanda za su fara daure ‘yan siyasa a Kano

Babban sufeton 'yan sandan Najeriya


Rundunar ‘yan sandan ta ce ‘yan siyasa na son tayar da husuma.

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano da ke Najeriy ta ce za ta soma daure ‘yan siyasar da ke amfani da kalaman batanci wajen cin mutuncin shugabanni ko junansu.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Magaji Musa Majiya ne ya bayyana wa BBC hakan lokacin taron masu ruwa da tsaki kan tsaftace kalamai a gidajen rediyo.

A cewar sa, `yan siyasar – wadanda aka fi sani da sojojin-baka – suna karewa juna tanaji maimakon su rungumi salon siyasa ba-da-gaba ba.

“Magana ake ta siyasa yadda za ka baje hajarka ba tare da cin tumunci da zagin mutane ba. Haka ne ya sa muka soma taro da shugabannin kafafen watsa labarai da sojojin-baka da kuma hukumar da ke sa ido a kafafen watsa labara, wato NBC. Mun yi zube-ban-kwarya, don haka babu sani babu sabo ga duk wanda ya karya doka,” in ji Majiya.
Sai dai wani dan siyasa, Malam Adamu Danjuma Wapa, ya ce ‘yan sandan sun mayar da su tamkar karamar katanga mai dadin ketara.

“Bamu taba ji an ce mun fadi kalamai masu kyau ba, kullum sai dai a ce mun fadi kalamai marasa dadi. Za ka ga mahukunta ba a cewa sun yi laifi; idan ana so a samu mafita, yadda na kasa zai yi laifi a hukunta shi, dole a hukunta na sama,” a cewaar dan siyasar.

Da ma dai ‘yan Najeriya na kokawa kan yadda ‘yan siyasa ke aike wa da sojojin-baka kafafen watsa labarai su rika cin mutuncin junan su.

More News

Ƴansanda sun kama muggan ƴan fashi da makami

Jami’an hukumar ‘yan sanda reshen Elemoro reshen jihar Legas sun kama wasu mutane uku da ake zargi da hannu a fashi da makami a...

An kama wasu mutane biyu da hodar ibilis a Lagos

Rundunar ƴan sandan jihar Lagos ta sanar da kama wasu mutane biyu da aka samu ɗauke da ƙunshin hodar ibilis mai yawan gaske. Mai magana...

Ƴan sanda sun kama wani mutum ɗauke da bindigogi 20 a Kaduna

Rundunar Æ´an sandan jihar Kaduna ta ce jami'anta sun kama wani  riÆ™aƙƙen mai safarar bindiga inda aka same shi da bindigogin AK-47 Æ™irar gida...

Kwankwaso ya bada tallafin miliyan ₦50 ga mutanen da ambaliyar Borno ta shafa

Tsohon gwamnan jihar Kano kuma jagoran jam'iyar NNPP, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya bada tallafin naira miliyan 50 ga mutanen da ambaliyar ruwa a...