
Rundunar yan sandan jihar Anambra ta ce jami’anta sun kama wani mutum mai shekaru 25 da nonon wata mata da aka cire a yankin Awada dake jihar.
A wata sanarwa da aka fitar ranar Litinin, Tochukwu Ikenga mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar ya ce wanda aka kama mai suna, Samuel Chukwueze ya shiga hannun jami’an tsaro a ranar 06 ga watan Yuli
Ikenga ya ce an karbi sashen jikin matar da aka samu tare da shi inda aka ajiye a dakin ajiye gawarwarki a yayin da ake cigaba da gudanar da bincike.
A wani samamen na daban jami’an rundunar sun kubutar da wani direban mota da aka yi garkuwa da shi tare da kwato kayan da kudinsu ya kai miliyan 9.5.
Ya ce an kama mutane uku Udegenyi Ugochukwu, mai shekaru 38; Anayochukwu Okonkwo, mai shekaru 47; da kuma Good Odigili, 47 inda ake zarginsu da aikata laifin.