
Rundunar yan sandan jihar Gombe ta ce jami’anta sun kama wani mutum da ake zargi da mallakar jabun dalar Amurka $1000.
A wata sanarwa ranar Laraba, Buhari Abdullahi mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Gombe ya ce jami’an ofishin yan sanda na Lawanti Airport ne suka kama Usman Kawu mai shekaru 35 a ranar 25 ga watan Yuni.
Abdullahi ya ce Kawu wanda ya fito daga kauyen Kunji Kwadon dake karamar hukumar Yamaltu-Deba an same shi da dala 100 guda 10 da suka kama $1000 kusan naira miliyan 1,500,000 a kudin naira da ake zargi na bogi ne.
“An samu wanda ake zargi da mallakar dalar Amurka da ake zargi ta jabu ce da ya yi yunkurin amfani da ita wajen yaudarar al’ummar da basu ji basu gani ba, ” a cewar sanarwar.
“Binciken farko da aka gudanar ya nuna cewa yana dauke da dalar Amurka guda 10 na yan $100 da ake zargin na jabu ne.”
Mai magana da yawun rundunar ya ce Kawu ya amsa laifinsa lokacin da ake masa tambayoyi inda ya yi ikirarin cewa wani da suke tare ne ya bashi kudin da aka ki bayyana sunansa.