’Yan Sanda Sun Kama Wani Mutum Da Ake Zargi Da Yin Lalata Da Fashi


Rundunar ‘Yan sandan Jihar Lagos ta sanar da kama wani mutum da ake zargi da aikata fyade da fashi a kan mata fasinjoji a sassa daban-daban na jihar. An bayyana wanda ake zargin da suna Adedayo Ben Adegbola.

Bayanan da suka fito daga Sashen Binciken Manyan Laifuka na ‘Yan sanda (SCID), Panti, sun tabbatar da cewa an kama Adegbola bayan dogon bincike mai amfani da bayanan sirri. An ce hoton wanda ake zargin ya yi yawo sosai a shafukan sada zumunta kafin kama shi.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Abimbola Adebisi, ya bayyana a cikin wata sanarwa da aka fitar ranar Asabar, 1 ga Nuwamba, 2025, cewa an kama Adegbola ne bisa umarnin Kwamishinan ‘Yan Sanda na jihar, CP Olohundare Jimoh, wanda ya bayar da umarnin a gudanar da cikakken bincike bayan korafe-korafen da mata da dama suka shigar.

A cewar sanarwar, an kama wanda ake zargin ranar Juma’a, 31 ga Oktoba, 2025, da misalin ƙarfe 9:40 na safe, bayan haɗin gwiwar jami’an bincike na SCID.

An kuma gano motar da ake zargin yana amfani da ita wajen aikata laifuffukan — wata jaƙar mota kirar Toyota Corolla mai lambar rajista JJJ 226 HT.

Sanarwar ta ce, “Wanda ake zargin yana hannun ‘yan sanda a halin yanzu, kuma ana ci gaba da bincike domin kama sauran abokan aikinsa da ake zargin suna da hannu cikin laifuffukan.”

Rundunar ta ce an adana motar da aka kwato a matsayin hujja, kuma za a gabatar da ita a kotu yayin shari’a.

An bukaci duk wata mace da ta taba fuskantar irin wannan hari ta kai rahoto zuwa ofishin SCID, Panti, domin bayar da bayanai da shaidu da za su taimaka wajen kammala bincike.

More from this stream

Recomended