Rundunar ‘yan sandan jihar Anambra ta cafke wani mutum mai suna Okwuchukwu Ezimuo, mai shekara 45, bisa zargin caka wa ‘dan uwansa wuka har lahira saboda rikicin filin iyali a garin Awka-Etiti, Idemili ta Kudu.
Kakakin rundunar, SP Tochukwu Ikenga, ya bayyana cewa mutumin da aka kashe, Joseph Dike, mai shekara 65, ya mutu ne bayan da aka kai masa duka a kirji lokacin sabani da ake yi kan fili a ranar Litinin da yamma.
An garzaya da shi asibiti bayan faruwar lamarin, inda likita ya tabbatar da mutuwarsa.
Ikenga ya ce jami’an rundunar sun kai ziyara wajen da abin ya faru, kuma sun tattara muhimman shaidu. Ya kara da cewa wanda ake zargin yana tsare a hannun ‘yan sanda kuma bincike yana gudana.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Ikioye Orutugu, ya roki jama’a da su rika warware sabani cikin lumana, ya kuma ba da umarnin a mika shari’ar ga sashen binciken manyan laifuka na jihar domin zurfafa bincike.
‘Yan Sanda Sun Kama Mutumin Da Ya Yi Ajalin ‘Dan Uwansa Na Jini
