Rundunar ‘Yan Sanda ta Jihar Yobe ta sanar da cewa jami’anta daga ofishin Fika sun kama wani matashi mai shekaru 22 bisa zargin yin fyaɗe ga yarinya ‘yar shekara 11.
Mai magana da yawun rundunar, SP Dungus Abdulkarim, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da aka fitar ranar Asabar.
Sanarwar ta ce wanda ake zargin ya yaudari yarinyar da sunan zai taimaka mata a gona tare da yi mata alƙawarin lada, sai kuma ya yi amfani da damar wajen aikata mummunan laifin.
A cewar rundunar, “A ranar 13 ga Satumba, 2025, da misalin ƙarfe 7 na safe, bayan samun kiran gaggawa daga mai kula da yarinyar a kauyen Maiduwa, karamar hukumar Fika, jami’an ‘yan sanda daga ofishin Fika suka cafke wani Ishiaku Bukar, mai shekaru 22, ɗan asalin yankin.”
Rundunar ta ƙara da cewa yayin bincike, wanda ake zargin ya amsa laifinsa.
“Bincike yana gudana, tare da gudanar da gwajin likita da kuma kula da lafiyar yarinyar da abin ya faru da ita,” in ji sanarwar.
Sai dai rundunar ta nuna damuwa kan yadda ake ƙara samun rahotanni na cin zarafi da fyade ga mata da ƙananan yara da ake ɗaukar su aikin gona. Ta kuma gargadi cewa duk wanda aka samu da hannu wajen aikata irin wannan mummunan laifi za a hukunta shi bisa ƙa’ida.
Kwamishinan ‘Yan Sanda na jihar, Emmanuel Ado, ya yi kira ga jama’a da su kasance masu sa ido tare da bayar da rahoto kan duk wani mutum da ke amfani da ayyukan gona wajen cin zarafi ko muzgunawa mata da yara.
Ya ce, “Ku ce a’a ga fyade, ku kare mata da yara.”
‘Yan Sanda Sun Kama Matashi Bisa Zargin Yi Wa Ƴar Karamar Yarinya Fyaɗe a Yobe
