Yan sanda sun kama masu safarar makamai a Katsina

Rundunar yan sandan jihar Katsina ta samu nasarar kama wasu masu safarar makamai ga yan fashin daji da suka addabi wasu sassa daban-daban na jihar.

Mutanen biyu sun fada hannun jami’an tsaron ne akan titin Ingawa zuwa Karkarku dake jihar ta Katsina.

Binciken farko da aka gudanar ya nuna cewa mutanen sun ɗauko makaman ne daga karamar hukumar Hadejia ta jihar Jigawa.

Bindiga kirar GPMG guda daya aka samu tare da su da harsashi na bindigar AK-47 guda 1036 da kuma harsashi kirar PKT guda 232.

Jihar Katsina na daya daga cikin jihohin arewa maso yamma dake fama da hare-haren bindiga dake jawo asarar rayuka da dukiyar al’umma.

More from this stream

Recomended