Rundunar ‘Yan Sanda ta ƙasa ta ce ta kama wasu jarkokin man fetur guda 103 da ake ƙoƙarin fitarwa zuwa Kamaru da Jamhuriyar Benin.
Mai magana da yawun rundunar, Benjamin Hundeyin, ya bayyana cewa “an kama jarkoki 60 a cikin mota Toyota Starlet a Mubi, Adamawa, yayin da sauran guda 43 da aka loda a kan babura uku aka kama su a hanyar da ke kaiwa Jamhuriyar Benin.”
Ya ƙara da cewa, “a Jibia, Katsina, wani mai babur ya tsere ya bar man da yake shirin kaiwa Nijar bayan ganin jami’an sintiri.”
A cewarsa, jami’an sun kuma gano bindigogi, kayan maye, da motocin da aka sato a jihohi daban-daban, tare da ceto mutane da ake ƙoƙarin safarar su zuwa ƙasashen waje ba tare da takardun izini ba.
Hundeyin ya jaddada cewa “wadannan ayyuka na nuna jajircewar rundunar ‘yan sanda wajen kare tsaron ƙasa da tattalin arzikin al’umma.”
‘Yan Sanda Sun Kama Mai Safarar Man Fetur Zuwa Ƙasashen Waje
