Yan sanda sun kama gawurtaccen mai safarar makamai a jihar Benue

Rundunar yan sandan Najeriya ta ce jami’anta sun samu  nasarar bankadowa tare da tarwatsa wasu gungun mutane dake samarwa da yan bindiga makamai a jihar Benue da sauran jihohin dake yankin arewa ta tsakiya.

Muyiwa Adejobi mai magana da yawun rundunar yan sandan Najeriya ya ce an samu wannan gagarumar nasara ne sakamakon namijin kokarin da sashen tattara bayanan sirri ne rundunar ke yi.

Ya ce gano mutanen da aka yi wani bangare ne na binciken da rundunar ta ke kan munanan hare-haren da ake kai wa kan al’ummomi  daban-daban a jihar Benue ciki har da harin da aka kai Yelewata.

Adejobi ya ce a ranar 21 ga watan Yuni na 2025  jami’an yan sanda bisa dogaro da bayanan sirri sun farma wata maboya dake cikin daji dake kan iyakar Kardako- Yelwata a jihohin Nasarawa da Benue.

Ya ce an yi musayar wuta har ta kai yan bindigar sun tsere da raunukan harbin bindiga ya kara da cewa an samu nasarar gano bindigogi kirar GPMG a wurin.

Ya cigaba da cewa a wani samamen na daban jami’an sun samu nasarar kama Abubakar Isa mai shekaru 25 akan hanyar Lafia- Makurdi inda yake dauke da bindigogi kirar AK-47 guda uku da kuma harsashi 1002.

More from this stream

Recomended