
Yan sanda a jihar Benue sun samu nasarar kama wani gawurtaccen dan bindiga da ake zargi da kai wasu hare-hare kan jami’an tsaro a jihar Benue.
Zagazola Makama masani dake wallafa bayanai kan sha’anin tsaro a yankin tafkin Chadi ya ce wanda ake zargin da aka bayyana da suna Yongu Justine Makwagh daga Kadarko a jihar Nasarawa an kama shi ne a Makurdi babban birnin jihar Benue bayan da jami’an tsaro suka shafe tsawon lokaci suna bibiyarsa.
Makama ya ce DPO din yan sanda na Daudu shi ne ya jagoranci kamen tare da karin jami’an tsaro daga runduna ta musamman ta babban sifeton yan sanda biyo bayan gamsassun bayanan sirri da suka sam
Ya kara da cewa Makwagh na daga cikin jerin sunayen wadanda jami’an tsaro suke nema ruwa a jallo kan zargin hannu da yake da shi a wasu jerin hare-hare da aka kai a yankin Sankera.
Ana ganin kamen wata babbar nasara ce a yakin da jami’an tsaro suke da yan bindiga a jihohin na Nasarawa da Benue.

