Yan sanda sun gano masana’antar bom a Anambra

Rundunar yan sandan jihar, Anambra ta ce jami’anta sun lalata wata masana’antar kera boma-bomai da ake amfani da ita a matsayin sansanin mayakan IPOB a Isseke dake karamar hukumar Ihiala ta jihar.

A wata sanarwa da aka fitar ranar Lahadi, mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar, Tochukwu Ikenga ya ce jami’an yan sandan sun kuma gano wasu bama-bamai a sansanin.

Ikenga ya ce jami’an sun lalata boma-boman ya kara da cewa daya daga cikin bom din da aka binne a wajejen sansanin ya fashe a lokacin samamen inda ya lalata wani titi sosai.

” An dana bomb din ne domin ya zama garkuwa ta hana jami’an tsaro isa sansanin kuma ba a samu asarar rai ba a lokacin samamen,” ya ce .

Ya ce sansanin na daya daga cikin manyan cibiyar mayakan  kungiyar ta yan aware da suke amfani da shi sama da shekaru biyu wajen tayar da hankali a jihar.

More from this stream

Recomended