
Rundunar yan sandan jihar Kebbi ta ce jami’anta sun ceto mutane uku da aka yi garkuwa da su a karamar hukumar Shanga ta jihar.
A wata sanarwa da aka fitar ranar Juma’a mai magana da yawun rundunar, Nafiu Ibrahim ya ce an ceto mutanen ne bayan wani samame na hadin gwiwa da jami’an tsaro suka kai.
Abubakar ya ce a ranar 27 ga watan Yuli da misalin karfe 02:00 na dare yan bindiga dake dauke da makamai sun mamaye kauyen Sangara dake Shanga inda su kayi garkuwa da mutane uku.
Ya ce baturen yan sanda na Shanga ya hada tawagar jami’an tsaro da suka hada da sojoji, yan sanda, civil defense, yan bijilante da kuma mafarauta inda suka kaddamar da aikin kubutar da mutanen.
“A lokacin da aikin ceto ke gudana sun bi sawun masu garkuwar har ya zuwa tsaunin, Shanga inda suka yi musayar wuta da su sosai, ” a cewar sanarwar.
“Sun yi garkuwa da wani Muhammad Namata mai shekaru 25, Gide Namata mai shekaru 20 da kuma Hamidu Alhaji Namani mai shekaru 35 dukkansu da suka fito gida daya,”
Sanarwar ta ce an ceto mutanen a ranar 31 ga watan Yuli da karfe 03:30 na rana bayan da masu garkuwar suka tsere da raunuka sakamakon amon wuta daga jami’an tsaro.