
Rundunar yan sandan jihar Benue ta ce jami’anta sun samu nasara ceto wasu fasinjoji 11 da aka yi garkuwa da su yan kwanakin da su ka wuce a karamar hukumar Okpokwu ta jihar.
A ranar 22 ga Yuni ne aka yi garkuwa da fasinjoji 13 har da direban motar ta kamfanin sufurin Benue Links mallakin gwamnatin jihar Benue a garin Eke-Elengbecho.
Motar na kan hayarta ne ta zuwa Makurdi daga garin Abeokuta na jihar Ogun lokacin da yan bindigar su ka tare ta.
Tun da farko dai an samu nasarar ceto biyu daga cikin fasinjojin wadanda tuni aka mayar da su cikin iyalansu.
A wata sanarwa da Udeme Edet mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Benue ya fitar a ranar Lahadi ya ce jami’an yan sanda sun samu labarin cewa masu garkuwar na shirin sauyawa mutanen matsuguni inda za su bi da su ta cikin kauyen Ondo dake yankin Ugbokolo na jihar Benue hakan ne ya sa a ka gano su a cikin daji.
“Bisa dogaro da bayanan sirrin da ke cewa masu garkuwar za su wuce da mutanen ta wata hanyar kafa ta cikin daji ta wajejen kauyen Ondo dake Ugbokolo karamar hukumar Okpokwu ya sa jami’ai su ka garzaya zuwa yankin suka gudanar da bincike mai zurfi,” a cewar sanarwar.
“Bayan shafe sa’o’i ana bincike a yankin an gano mutane 11 tare da kubutar da su lafiya.”
Sanarwar ta kara da cewa an samu nasararar kama mutum guda da ake zargi na da hannu a yin garkuwa da mutane.