‘Yan sanda na bincike kan Salah

[ad_1]

Na’urarku na da matsalar sauraren sauti

Bidiyon da aka nuna Mo Salah yana taba waya kuma yana tuki

Kungiyar Liverpool ta sanar da ‘yan sanda game da wani hoton bidiyo da aka dauka na Mohammed Salah yana dannar wayar salula yayin da yake tukin mota.

Rundunar ‘Yan sandan yankin Merseyside ta tabbatar a wata sanarwa da ta wallafa a Twitter cewa an gabatar da bidiyon a sashen da ya dace domin bincike.

Liverpool ta ce ta sanar da ‘yan sanda ne bayan ta tattauna da dan wasanta.

Ta kara da cewa duk wani mataki da za ta dauka kan dan wasan na Masar za ta dauke shi ne a cikin gida.

Bidiyon wanda ya mamaye shafukan sada zumunta ya nuna Mo Salah wanda ya jefa wa Liverpool kwallaye 44 a raga a kakar da ta gabata yana dannar waya a gaban motar da magoya bayansa suka mamaye kuma yana tuki.

Liverpool ta ce ba za ta sake cewa komi ba game da batun haka ma dan wasanta Salah.

[ad_2]

More News

NDLEA ta kama tan 761,000 na miyagun kwayoyi cikin shekaru 3

Shugaban hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA, Buba Marwa, ya ce hukumar ta kama tan 761,000 na haramtattun kwayoyi...

An saka jirage uku na  shugaban Ć™asa a kasuwa

Gwamnatin Najeriya ta saka jiragen shugaban ƙasa guda uku a kasuwa a wani yunkuri da mahukunta suka bayyana da cewa zai rage yawan kuɗaɗen...

Ćłan bindiga sun kashe mai POS a Ekiti

Wasu Ć´an bindiga sun kashe wani mai sana'ar POS a garin Ado-Ekiti babban birnin jihar Ekiti. Mai sana'ar ta POS dake da suna Alfa Taofeek...

Har yanzu Sanusi ne sarkin Kano—Gwamnatin Kano

Gwamnatin jihar Kano ta ce hukuncin da wata babbar kotun tarayya karkashin jagorancin mai shari’a Abdullahi Muhammad Liman ta yanke a safiyar ranar Alhamis...