
Rundunar yan sandan jihar Kaduna ta ce jami’anta sun kama Mati Bagio wani gawurtaccen dan bindiga da ya shafe shekaru 11 ana nemansa ruwa a jalllo.
Mansir Hassan mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Kaduna a wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a ya ce an kama wanda ake zargin mai shekaru 34 a gidansa dake Unguwar Galadima a garin Shika na karamar hukumar Giwa ta jihar Kaduna.
Hassan ya ce wanda aka kama din jagorancin gungun yan ta’adda da su ka kai munanan hare-hare da dama a kananan hukumomin, Giwa, Hunkuyi, Faskari, Faskari, Dandume da kuma Funtua dake jihohin Katsina da Kaduna.
Ya ce yan sanda sun samu bindiga kirar AK-47 guda daya, AK-47 kirar gida guda daya, bindingar Pump Action guda daya da kuma karamar bindiga Pistol guda biyu a tare da shi.
Sauran makaman da aka samu tare a shi sun hada da gidan harsashin bindigar Ak-47guda biyu, harsashin Pistol guda 87, hannun AK-47 kirar gida guda 10 da adda da kuma sauran kayayyaki.
“Wannan kamen wata babbar nasara ce a kokarin da muke na kawar da batagari da kuma kawar da haramtattun makamai daga cikin al’ummomin mu,” a cewar sanarwar.
Sanarwar ta kara da cewa ana cigaba da gudanar da bincike domin kawo ragowar sauran batagarin dake taimaka masa wajen aikata barna.