
Rundunar yan sandan birnin tarayya Abuja, ta ce jami’an ta sun kama wani yaro mai shekaru 16 da ake zargi da kashe mahaifinsa.
Kwamishinan yan sandan birnin tarayyar, Haruna Garba shi ne ya bayyana haka lokacin da yake ganawa da manema labarai.
Ya ce wanda ake zargi ya kashe mahaifinsa ne ta hanyar amfani da taɓarya.
A cewar kwamishinan lamarin ya faru ne lokacin da mahaifiyar wanda ake zargi da kuma mahaifinsa suka rikice da faɗa a a tsakaninsu inda Wanda ake zargin ya shigarwa mahaifiyarsa inda yayi amfani da taɓarya ya daki mahaifin nasa a kansa da karfi inda hakan ya yi sanadiyar mutuwarsa.