- Daga Nduka Orjinmo
- BBC News, Abuja
Shlomo Ben Yaakov ke nan rike da littafin Attaura, yana karanto ayoyi daga cikinsa, a wani wurin ibada irin na Yhudawa, da ke wajen babban birnin tarayyar Najeriya Abuja.
Shi ne limamin masu ibadar, yana karatun ne cikin murya mai dadi da harshen Hibru, bayan ya karanta, gomman masu binsa suma su maimata.
Sai dai yawancin mabiyan ba su ma san harshen ba sosai, to amma, duk da rashin yawan wannan al’umma a Najeriya, mabiyan na cewa suna da alaka ta kaka da kakannin da Yahudawa, ta tsawon shekaru daruruwa.
Amma kuma duk da wannan ikirari mutanen na cike da damuwa da fushi ganin cewa Isra’ila ba ta dauki wannan ikirari nasu da muhimmanci ba, domin ba ta damu da su ba.
“Ina daukar kaina a matssayin Bayahude,” in ji Mista Yaakov.
A kofar dakin ibadar na wadannan mabiya da ke ikirarin su Yahudawa ne a (Gihon Hebrew Synagogue) a kauyen Jikwoyi da ke wajen babban birnin tarayyar Najeriya Abuja. Ga wani teburi nan ana iya gani an kafa shi a cikin wata rumfar tanti da aka yi da ganyen itacen kwakwa, domin bikin ibadar Yahudwa (Sukkot), da ake yi domin tunawa da shekarun da Yahudawa suka shafe a hamada a kan hanyarsu ta zuwa kasar da suka ce Allah Ya yi musu alkawari (Falasdinu)
“A daidai wannan lokaci da muke wannan biki can a Isra’ila ma ana yin bikin a yanzu,” In ji Mista Yaakov, yayin da mabiyan ke raba burodi, wanda aka yi a wurin ibadar da kuma giya a wasu kananan kofuna.
Mista Yaakov, ɗan kabilar Igbo ne – ɗaya daga cikin manyan kabilu uku na Najeriya, daga yankin kudu maso gabashin kasar. Sunansa na gargajiya Nnaemezuo Maduako.
Ƴan kabilar Igbo da dama sun yi amanna cewa suna da jinin Yahudawa, a matsayin ɗaya daga cikin kabilu goma na Isra’ila da suka ɓata, ko da yake yawancinsu ba sa yin addinin na Yahudawa, kamar yadda Mista Yaakov ya ke yi. Masu yin ibadar ƴan kadan ne, domin suna kasa da ɗigo ɗaya ne cikin kashi ɗari na yawn ƴan kabilar Igbo miliyan 35 da aka yi kiyasin akwai.
Su waɗannan kabilu goma, an ce sun ɓace ne bayan da aka kama su aka tsare, lokacin da aka kama daular arewacin Isra’ila a karni na 8 kafin zuwan Annabi Isa (AS). Ana daukar yahudawan Habasha a matsayin ɗaya daga cikinsu.
Al’adun kabilar Igbo kamar su kaciya da zaman makoki na tsawon kwana bakwai da murnar komawar sabon wata da bikin aure, waɗanda duk ake yi a karkashin runfunan na kara tabbatar da wannan ikirari da suke yi cewa sun da alaka da Yahudawa.
‘Babu wata alama ta tabbatarwa‘
To sai dai duk da wannan ikirari na alaƙa da Yahudawa da kabilar ta Igbo ke yi Chidi Ugwu, wani masanin tarihi da halayar dan adam a jami’ar Najeriya da ke Nsukka, a Enugu ya ce wannan ikirari na alaƙa da Yahudwa ya fara ne bayan yaƙin basasa na Biafra.
Ƴan kabilar Igbo sun dade suna kokarin ɓallewa daga Najeriya, inda suka yi rashin nasara a mummunan yaƙin da aka yi a tsakanin 1967 zuwa 1970.
Masanin ya ce wasu mutanen suna neman wani abu ne da zai karfafa musu zuciya, saboda haka ne suka fara wannan ikirari na alaka da Yahudawa.
Sun ɗauki kansu a matsayin mutanen da aka muzgunawa, kamar yadda aka yi wa Yahudawa a tarihi, musamman a lokacin kisan kiyashi.
“Cin mutunci ne a kira Igbo wata kabila da ta bace ta wata al’umma, babu wata shaida ta tarihi ko wadda aka tono a kasa da ta tabbatar da haka,” ya gaya wa BBC.
Sai dai ya ce kamar yadda shaida ta nuna ƴan kabilar Igbo na daga cikin wadanda suka yi hijira daga Masar dubban shekaru da suka wuce, wannan ne ya sa yake ganin Yahudawa suka ari wasu al’adu na Igbo lokacin da suka je can.
Shekaru da dama da suka wuce an yi ta kokarin yin gwaji na ƴaƴan halita domin tabbatar da alakar ta Igbo da Yahudawa, amma ba a ga wata alama ba.
Haka shi ma (limamin yahudawa) Rabbi Eliezer Simcha Weisz, shugaban harkokin kasashen waje na limamin Yahudawa na Isra’ila, hukumar da ke tabbatar da alakar duk wata kabila da Yahudawa ya nuna tababa a kan ikirarin ƴan kabilar ta Igbo, a hirarsa da BBC
Ya ce sai dai idan yahudawan na Najeriya sun sauya ne suka koma bin addinin Yahudawa, wanda wannan abu ne da ya kunshi abubuwa na ibada da yawa da kuma bayyana gaban wata kotu, wadda kuma babu ita a Najeriya, to ba za a taba daukarsu a matsayin Yahudawa ba.
Mista Yaakov na daukar maganar bin wannan mataki na sauyi a matsayin muzantawa.
Ya ce idan suka tafi a matsayin wadanda suka sauya addini to ba za a ɗauke su a matsayin cikakkun ƴan kasa ba a Isra’la, za su zama baya a dangi.
Karuwar masu neman ɓallewa
Masu ibara Yahudawan a wannan wuri na Abuja (Gihon) sun dauki maganarsu da gaske, domin su da wasu ƴan Najeriyar kusan 12,000 da ke yin wannan ibada na samun goyon baya daga wasu Yahudwan ƴan gargajiya a faɗin duniya, wadanda suke ba su tallafi da kawo musu ziyarar goyon baya har ma da kokarin ganin sun samu karɓuwa.
Shi kam yana daga cikin masu ra’ayin cewa sun zo ne daga Moroko shekara 500 baya, da farko suka sauka a Timbuktu kafin su sake nausawa kudu, kuma yana fatan cewa wata rana za su samu karɓuwar da ya kamata su samu. Kamar yadda ya fada a hirarsu da BBC.
Yanzu dai wannan wurin ibada na Yahudawa da ke Abuja yana da hadakar kabilu daban-daban, da suka kai mutane sam da 40 da ke halarta.
The first time Ipob emerged, I cried at the synagogue”
Sai dai kuma wadanda suka dade tare kuma da fice a bin addinin na Yahudawa a Najeriya ba sa daukar mabiyansa a matsayin ainahin cikakkun Yahudawa, domin wasu mabiyan nasa na haɗa addinin da kuma wasu nau’ukan ibada na Kiristanci.
Yanzu dai Kanu yana tsare inda yake fuskantar shari’a kan laifin cin amanar kasa, kuma hukumomi sun haramta kungiyarsa ta Ipob, wadda ta dauki makamai a kwanan nan a matsayin kungiyar ta’addanci.
Mista Avichai, wanda tsohon sojan aware na Biafra ne ya ce, “Lokacin da, Ipob ta bayyana da farko, na yi kuka a wurin ibadar. Na ce: ‘Wannan yaron ya zo ya kawo mana matsala, saboda abin da yake yi ba dole ba ne,'”
Yana fargaba cewa abubuwan da kungiyar Ipob ke yi barazana ne ga al’ummomi 70 ko kusa da haka da ke addinin na Yahudawa wadanda ba ruwansu da siyasa a Najeriya.
A farkon wannan shekara an kama wata shugabar mabiya addinin na Yahudawa a yankin kudu maso gabashin Najeriya aka ɗaure ta tsawon wata ɗaya bayan da wasu daga Isra’ila suka ziyarci wurin ibadar.
Bakin sun zo ne domin su dauki hoto bidiyon rabon littattafan Attaura, wadanda suna da matukar tsada a cewar mabiyan na Najeriya sun iya siya, to amma sai aka yi zargin suna da alaƙa da kungiyar Ipob, saboda haka aka fitar da su daga kasar.
Wani mai addinin a majami’ar Gihon, ya gaya min cewa Nnamdi Kanu ne ya ja hankalinsa ya shiga, to amma gwagwarmayar da kungiyar Ipob ke yi yanzu da makamai ta saɓa wa akidar addinin.
Mista Yaakov ba shi da sha’awa a kan siyasar da ke tattare da kasancewa mai bin addinin yahudawa, abin da ya fi ba muhimmanci a wurinsa shi ne fannin addinin.
Idan hukumomin Isra’ila suka amince da wadannan ‘yan kalilan din mabiya addinin na Yahudawa ƴan kabilar Igbo na Najeriya, kamarshi, hakan zai sa su samu karɓuwa sosai a Najeriya. Misali a yanzu babu wani babban limamin Yahudawa kuma samun kayan addinin a Najeriya na da wahala.
Mista Yaakov zai so ya samu horo ya kuma zama limamin yahudawa na farko na Najeriya, wanda wannan abu ne da sai ya yi karatu a makarantar koyon limanci ta addinin na Yahudawa ko kuma a karkashin wani kwararren limamin.
Ya ce “Ga mu da muka san tushenmu, muna da kwarin guiwa a kan abin da muke bi.”
“Idan Kiristoci da Musulmi za su iya karbar nasu su kuma tallafa musu, to ina ganin Yahudawa ma ya kamata su nuna goyon baya da bayar da kwarin guiwa.”