‘Yan Najeriya Uku Sun Shiga Hannun Jami’an Tsaro a Delhi Bisa Zargin Damfarar Wata Mata

Rahotanni daga jaridar The Times of India a ranar Asabar sun bayyana cewa, rundunar ‘yan sandan yaki da laifukan intanet ta cafke wasu ‘yan Najeriya uku, Lezhu John, Gibril Mohammed, da Egboola Ekena, bisa zargin damfarar wata Ba’indiya.

Duk da cewa ba a gurfanar da su a gaban kotu ba tukuna bincike ya nuna cewa idan aka same su da laifi, suna iya fuskantar hukuncin zaman gidan yari na aƙalla shekaru uku, bisa doka ta Information Technology Act (2000) da dokokin Indiya na manyan laifuka.

A cewar Sashe na 66D na dokar Indian IT Act, wanda aka zayyana a shafin wata babbar kotu mai suna S.S. Rana & Co., “Duk wanda ya yi damfara ta hanyar yin kama da wani ta amfani da kayan sadarwa na kwamfuta, zai fuskanci hukuncin zaman gidan yari na shekaru uku ko kuma tara har zuwa rupis ɗari ɗaya.”

An zargi waɗannan mutanen uku da jagorantar wata ƙungiyar damfara ta yanar gizo da ta yaudari mutane da dama a faɗin Indiya.

Jami’an ‘yan sanda sun ce, lamarin ya faro ne lokacin da wata mace ta kai rahoto ga rundunar yaki da laifukan intanet, bayan ta gano cewa wani wanda ta haɗu da shi a shafin Instagram ya yaudare ta.

An gano hotuna da dama na maza da mata a cikin wayoyin salula na waɗanda ake zargi, waɗanda ake zargin suna amfani da su wajen ƙirƙirar bayanan ƙarya na kafafen sada zumunta domin yaudarar mutane.

More from this stream

Recomended