
Yan majalisar wakilai ta tarayya guda 6 ne suka sauya sheka daga jam’iyar PDP ya zuwa APC.
Har ila yau wasu yan majalisar biyu sun tsallaka jam’iyar PDP daga jam’iyar Labour Party.
Sanarwa sauya shekar ta su na kunshe ne cikin wata wasika da shugaban majisar, Tajuddeen Abbas ya karanta a yayin zaman majalisar na ranar Talata.
Obetta Chidi wanda ke wakiltar mazabar Nsukka/Igbo Eze south a jihar Enugu ya sauya sheka daga jam’iyar Labour Party ya zuwa PDP.
Shima Denis Agbo dake wakiltar mazabar Igbo Eze north/Udenu a jihar Enugu ya fice daga Labour Party ya zuwa PDP.
Victor Nwokolo dake wakiltar mazabun Ika north east/Ika south a jihar Delta ya fice daga jam’iyar PDP inda ya koma PDP.
Julius Pondi dake wakiltar mazabar Burutu ya fice daga jam’iyar PDP ya zuwa APC.
Thomas Ereyitomi wanda ke wakiltar mazabar Warri north/Warri south/Warri west ya fice daga PDP ya zuwa APC.
Sauran wadanda suka sauya shekar daga PDP zuwa APC sun hada da Nicholas Mutu, Okhodiko Jonathan da Ezechi Nnamdi dukkaninsu suna wakiltar al’ummomi daban na jihar Delta a majalisar wakilan.
Yan majalisar sun bayyana rikicin cikin gida da yaki ci yaki cinyewa a jam’iyunsu da kuma rabuwan shugabanci a matsayin dalilin sauya shekar ta su.